Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum 14 Da Ake Zargi Da Hannu A Kutsen Gidan Mai Shari’a Odili


'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Rundunar yan sandan Najeriya ta sami nasarar kama mutane 14 da ake zargin suna da hannu a kutsen da aka kai gidan babbar jojin kotun koli, mai shari’a Mary Odili, da ke birnin Abuja a ranar Alhamis.

Hadimin hulda da jama’a na shelkwatar rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yayin da ta ke holin mutanen a birnin Abuja.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin sun hada da wani babban jami’in ‘yan sanda na bogi, Lawrence Ajodo, edita wanda ya yi shelar cewa ya na ba da gudummawa a jaridar This Day, Stanley Nkwazima, da kuma wani da ya ce shi malamin addinin Islama ne, Ali Umar Ibrahim.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Frank Mba, ya bayyana wadanda ake zargin a birnin Abuja, inda ya ce kama mutanen ya biyo bayan wani binciken gaggawar da ‘yan sanda suka yi. don gano wadanda suka aikata aika-aikar.

Kazalika, Frank Mba ya ce akwai akalla wasu mutane goma da suka gudu wadanda ake zargi da hannu a cikin lamarin da suka hada da jami’an soji biyu.

A yayin gudanar da aikin binciken, ‘yan sanda sun gano cewa wani Aliyu Umar Ibrahim, wanda aka fi sani da kwarmata bayanan sirri da ba’a tabbatar da gaskiyar hakan ba ya fara fito da bayanin don a fallasa.

Daga bisani aka gano cewa ya sami labarin akwai makudan kudin irin na waje da aka ajiye a gidan mai shari’a Odili daga wani Yusuf Adamu, wanda ya bayyana kansa a matsayin uban gidansa ne Cif Peter Odili, a gida da ke lamba 7, titin Imo River, a unguwar Maitama.

Lamarin da ya kai ga tawagar kwato kudin gwamnati na bogi ta fara aiwatar da tsare-tsare da nufin kwato wadannan kudaden ba bisa ka’ida ba, don haka tawagar ta tuntubi wani Bashir Musa ma’aikacin babban bankin Najeriya wato CBN, wanda shi kuma ya nemi taimakon wasu mutane biyu wato Shehu Jibo da Abdullahi Adamu.

Kamen mutanen dai shi ne na baya bayan nan tun bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wa gidan mai shari’a Odili kawanya a unguwar Maitama.

Lamarin ya janyo suka daga bangarori da dama da suka hada da kungiyar lauyoyin Najeriya wato NBA, gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana, da dai sauransu.

Gwamna Wike ya baiwa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 domin ta kama wadanda suka aikata wannan aika-aika kuma ya yi ikirarin cewa lamarin wani yunkuri ne na kashe iyalin mai shari’a Odili.

A halin da ake ciki, babban sufetan yan sanda, Usman Alkali, ya sha alwashin yin taka-tsan-tsan wajen gurfanar da mutane 14 da aka kama wadanda ake zargi da aidata laifin.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, Frank Mba ya sanya wa hannu, rundunar ‘yan sandan ta ce ta kwato motoci uku da kwamfutar tafi-da-gidan ka da na’ura mai kwakwalwa na printer da flash drive da ake amfani da su wajen kera katin shaida na bogi daga hannun wadanda ake zargin.

Tuni dai ma’aikatar shari’a ta nesanta kanta da mutanen da ke karyar cewa ministan shari’a ya saka su aiki kwato kudadden da ake shelar cewa suna ajiye a gidan mai shar’a a Odili.

XS
SM
MD
LG