Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Damke Wani Mutum Da Matarsa A California


Louise Anna Turpin
Louise Anna Turpin

Hukumomi a Jihar California dake yammacin Amurka sun ce sun kama wani mutum da matarsa sakamakon samun su da lafin daure 'ya'yansu 13 a matsayin fursnunoni a muhalli mai tsananin kazanta.

Hukumomi a Jihar California dake yammacin Amurka sun ce sun kama wani mutum da matarsa sakamakon samun su da lafin ajiye 'ya'yansu 13 a matsayin fursuna cikin kazantaccen muhali.

Ana tsare da David Turpin da matarsa Louise Anna Turpin a kurkuku, har sai sun samu mai iya yin belinsu a kan kudi dala miliyan tara, yayin da 'yan sanda ke ci gaba da bincike akan tozartawa da saka yara cikin hadari.

'Yan sanda sun damke mutanen biyu a bayan da daya daga cikin 'ya'yansu mai shekaru 17 da haihuwa, ta samu halin tserewa daga gidan, ta kuma kira 'yan sanda na garin Perris dake kusa da birnin Los Angeles.

'Yan sandan suka ce yarinyar mai shekara 17, ta fi kama da 'yar shekara 10, a saboda mummunar ramar da ta yi a dalilan yunwa da rashin kulawa.

Sabanin yara 12 da 'yan sandan ke tunanin za su ceto, sai suka ga cewa wasu daga cikinsu ma 'yan shekara 18 ne zuwa 29.

Yan sandan sun bayyana cewa karamar cikin yaran 'yar shekara biyu ce, kana an daure wasu daga cikin yaran da sarka da kwado a jikin gado.

Wata sanarwar 'yan sanda ta bayyana cewa iyayen yaran ba su bayar da wani dalili na saka 'ya'yansu cikin wannan matsanancin halin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG