Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 2, Sun Kuma Ceto Mutane 7 Da Dabbobi 142 A Jihar Katsina


'Yan sandan Najeriya

Tawagar rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar dakile farmakin 'yan ta'adda masu yawa, wadanda ke tare mutane su yi musu fashi a titin Zango zuwa Kankara dake jihar ta Katsina,

Rundunar ta kuma yi nasarar kashe wani da ake zargi dan ta’adda ne da kuma kubuto da mutane takwas ciki har da kananan yara hudu da aka yi garkuwa da su.

Kazalika rundunar ta yi nasarar kwato shanu guda 82 da tumaki 70 da bindiga kirar AK-47 guda daya daga hannun yan ta’addan.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, shi ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a hedkwatar su dake Katsina a jiya Alhamis, inda aka bayyana wadanda aka ceto da gawar dan ta’addan da kuma bindigar da aka kwato.

Yan sandan Najeriya
Yan sandan Najeriya

Haka zalika, DPOn Kankara ya jagoranci tawagar 'yan sanda wajen dakile farmakin 'yan ta'addan dake addabar kauyen Fuloti da Gandu Karfi a karamar hukumar Malumfashi bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin.

Bayan musayar wuta da 'yan ta'addan, 'yan sandan sun yi nasarar sheke daya daga cikin hatsabiban, bayan sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da yara da mata masu shayarwa guda hudu.

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG