Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Najeriya

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani DPO a Jihar Katsina


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin DPO a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina a wani farmaki da suka kai a garin Magama da safiyar Laraba.

'Yan bindigar sun kai harin ne da karfe 2 na daren Laraba, inda suka kashe DPO Abdullahi Rano da kuma wani soja, bayan haka wani jami'in tsaron ya jikkata sakamakon harbin bindiga.

Wakilin magaji Mazanyar Magama, Abubakar Magaji, ya bayyana cewa a cikin daren makwabcin sa Alhaji Halliru ya kira shi ta waya ya fada masa cewa 'yan bindiga na unguwar, daga baya 'yan bindigar suka tafi da mai dakin Alhaji Halliru suka kuma yi awon gaba da wasu makudan kudi a gidansa.

A lokacin da ya je kai dauki bayan samun sakon halin da ake ciki ne 'yan bindigar suka yi wa tawagar DPO Rano kwanton bauna inda suka kashe shi da wani soja suka kuma harbi wani sojan a kafa, a cewar Malam Magaji.

Garin Magama, wanda ya hada iyaka da jamhuriya Niger wuri ne da ake hada-hadar kasuwanci a karamar hukumar Jibia.

Nan take dai jami'an tsaro ba su ce komai ba game da harin hakazalika maharan su ma basu tuntubi kowa ba tukun.

Saurari cikakken rahoton Sani Shu'aibu Malumfashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG