Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Harbe Wani Mutun Har Lahira A Filin Jirgin Sama


An harbe wani mutum har lahira a yau Asabar bayan da ya kwace Bindigar wani soja dake gadi a filin jirgin saman Orly dake Paris, a cewar ‘Yan sanda da kuma wadanda abin ya faru akan idonsu.

Jami’ai sun kwashe maziyarta a yayinda 'Yan sanda suke bin diddigin lamarin. Motocin ayyukan gaggawa sun kewaye filin jirgin yayinda matafiya da suke a rude suka taru a wurin ajiye motoci, sannan su kuma zaratan 'yan sandan kasar suka yi kokarin tabbatar da tsaron filin jirgin.

Jami’an Yan sandan Faransa sunce mutum daya ne ke da hannu a harin yayin da suka karyata rahotannin da suke cewa akwai mutum na biyu.

A wani bangaren kuma An harbi wani jami’in dan sanda da ji masa rauni a wajen duba motoci akan hanya a garin Stains, dake Arewa maso gabas da birnin na Faris a yau asabar kamar yadda ‘Yan sanda suka bada rahoto. Amma Jami’an ‘yan sandan na tarayya sunce babu wata alama da ta hada al’amarin da ya faru a filin jirgin sama na Orly da kuma Harbin Dansanda a garin Stains.

Wani mutum da alamarin ya faru a idonsa ya fadawa gidan talabijin na BMF cewa "Sojoji sunauna wannan mutumi wanda shi kuma ya auna bindigar da ya kwace akan Sojojin biyu da sukatinkare shi.

Wani shaida dabam kuma, ya fadawa BFM cewa Sojoji uku ne mutumin ya auna da bindigar, wadanda suka yi kokarin lallashinsa da ya ajiye. Daga nan shaidar ya ce ya ji karar harbi sau biyu.

Filin jirgin sama na Orly dai shine na biyu mafi girma bayan filin jirgin sama na Charles de Gaulle, ana zirga zirgar jiragen cikin gida da kuma na kasashen waje, musanman ma domin zuwa cikin turai da kuma Afirka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG