Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Tsohon Shugaban Barcelona, Bartomeu


Josep Maria Bartomeu

‘Yan sanda a kasar Spain sun kai samame a kungiyar kwallon kafar Barcelona, inda suka kama wasu manyan jami’an kungiyar Oscar Grau, da kuma Roman Gomez Ponti, jagoran lauyoyin kungiyar.

Haka kuma an cafke tsohon shugaban kungiyar ta Barcelona Joseph Maria Bartomeu, da na hannun damansa Jaume Masferrer.

An kama jami’an ne bisa zargin tafiyar da lamurran kungiyar ba bisa ka’ida ba, aikata ayukan cin hanci da rashawa da kuma wawure kudaden kungiyar, bayan da suka biya wasu kudade da kadan-kadan, domin kaucewa dokokin kula da hada-hadar kudade na cikin gida.

Wannan na zuwa ne kuma a daidai sa’adda ake ci gaba da gudanar da bincike akan badakalar kudade a kungiyar ta Barcelona, inda ake zargin jami’an kungiyar da kaddamar da gangamin bata sunan wasu ‘yan wasn kungiyar na da da na yanzu, kamar Lionel Messi, Gerrard Pique, Pep Guardiola da sauransu, wadanda suka soki lamirin yadda Bartomeu ya tafiyar da lamurran kungiyar.

Bartomeu da sauran jami’an hukumar sa ta gudanarwa, sun yi murabus daga mukamansu a ‘yan watannin da suka gabata, sakamakon cece-kucen da suka taso.

To sai dai Bartomeu ya dade yana musanta zargin almundahanar ta Barca, da aka kwashe tsawon watanni 12 ana bincike akai.

A wani labarin kuma mai fatan kasancewa sabon shugaban kungiyar ta Barcelona Joan Laporta, ya lissafa da kocin Arsenal Mikel Arteta, a zaman wanda zai maye gurbin kocin kungiyar Ronald Koeman.

Mikel Arteta
Mikel Arteta

Laporta ya bayyana karara cewa, yana ra’ayin Koeman ya ci gaba da zamansa a kungiyar, to amma ya ce in ma wani abu ya sa ya bar aiki a kashin kan sa ko kungiyar ta kore shi, to yana goyon bayan kocin na Arsenal da ya maye gurbinsa.

Ronald Koeman, Sabon Kocin Barcelona
Ronald Koeman, Sabon Kocin Barcelona

Tuni dai da Laporta, wanda tsohon shugaban kungiyar ne, ya bayyana wadanda zai yi aiki da su idan ya sami lashe zaben shugabancin kungiyar da za’a gudanar a cikin watan nan.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG