Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Wasu Masu Zanga-zanga a Rasha


‘Yan sandan Rasha sun kama masu zanga zanga da dama ciki har da ‘yan adawa a wata zanga zanga da aka yi a jiya Lahadi, bisa bukatar dora masu takaran ‘yan adawa a kan takardar zabe a birnin Moscow, da za a gudanar a cikin watan Satumba.

Sama da mutane dubu suka taru a dandalin Pushkin Square biyo bayan sakwanni da aka turawa jama’a a kan shafukan sada zumunta a kan wannan taron.

Wata kungiyar sa ido a kan zanga zanga ta ce an kama mutane 38 a cikin macin da ake ganin an yi shi cikin lumana. Wasu masu zanga zangar sun yi ihu a kan ‘yan sanda suna ce musu kada su kunyatar da rigar sarki da kuke saye dasu, lamarin da yasa jami’an tsaron suka abkawa taron da hukumomi ke gani ya sabawa doka.

Masu zanga zangar sun yi maci ne zuwa ofishin magajin garin birnin Moscow da kuma helkwatan hukumar zabe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG