Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Sanda Sunyi Awon Gaba Da Shaharraren Mawaki Bobi Wine


Ugandan pop star turned opposition MP, Robert Kyagulanyi, is helped by his supporters as he delivers a speech outside his home in Kampala, Uganda, after returning from the United States on Sept. 20, 2018.
Ugandan pop star turned opposition MP, Robert Kyagulanyi, is helped by his supporters as he delivers a speech outside his home in Kampala, Uganda, after returning from the United States on Sept. 20, 2018.

Alhamis Shaharraren Mawaki, kuma dan Majalisa Bobi Wine ya koma Kampala inda yan sandan kasar Uganda suka damke shi a filin saukar jiragen sama na kasar.

Dan majalissar, dan adawar kasar Uganda, kuma shaharraren mawaki Bobi Wine, yan sanda sun tare shi a yau Alhamis lokacinda ya sauka a filin jirgin saman Kampala, suka yi awon gaba da shi.


An hana yan jaridu shiga cikin filin jirgin kuma aka tsaurara matakan tsaro a birnin Kampala, a yayinda aka tura jami’an tsaro akan titunan birnin. Jiya laraba ‘yan sanda suka hana mutane yin gangami a gaban filin saukar jirage da wasu wurare domin tarbar mawakin dan shekaru 36.

Kafofin yada labarum kasashen waje dana kasar da kuma dandalin sada zumunci na yanar gizo sun bada rahoton cewa, dan-uwan mawaki Wine da manajan sa da kuma mawakan sa suma an kama su, a lokacin da suka sauka daga cikin jirgin bayan sun fito daga Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG