Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Da 'Yan Shi'a Sun Yi Arangama a Yini Na Biyu


Zanga zanga domin a sako shugaban mabiya Shiya, Shaikh Ibrahim El-zakzaky wanda yake tsare tun shekarar 2015

Mabiya Mazhabar Shi'a a Najeriya sun ci gaba da yin taho mu gama da 'yan sanda a Abuja a kokarinsu na ganin an sako shugabansu Ibrahim El Zakzaky wanda yake tsare tun a 2015.

‘Yan sanda a Najeriya, sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla a yini na biyu da suka kwashe suna arangama da mabiya Mazhabar Shi’a, a Abuja, babban birnin kasar.

‘Yan Shi’ar suna zanga zanga ne domin neman a saki shugabansu, Malam Ibrahim El Zakzaky, wanda hukumomi suka kama shi tun a watan Disambar 2015.

Daya daga cikin jagororin kungiyar fararen hula ta “Concerned Nigerians," Deji Adeyanju, wanda shi ma ya shiga zanga zangar, ya ce ‘yan sandan sun kama mutane da dama, yana mai jaddada cewa “idan suka ci gaba da kai musu hari, su ma za su ci gaba da fitowa.”

Sai dai jami’an tsaron ba su ce uffan ba dangane da wannan zanga zanga da aka yi a jiya Talata.

Malam El Zakzaky, ya kasance a hannun hukumomin kasar, tun bayan wata arangama da mabiyansa suka yi da dakarun Najeriya a birnin Zaria a watan Disambar 2015.

Ya kuma ci gaba da kasancewa a tsare, duk da wani umurni da wata kotu ta bayar na a sake shi.

A ranar Litinin ma, an yi makamanciyar wannan arangama a birnin na Abuja, lamarin da ya kai ga tsare akalla mutum 115.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG