Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Jamus Sun Harbe Wani Mutumi Da Ya Kade Mutane Da Mota


'Yan sanda a Heidelberg, dake kasar Jamus sun harbe tare da jiwa wani mutum rauni a yau Asabar bayan mutumin ya kade mutane har uku da mota.

Mutumin ya tuka motar ne cikin taron mutane a wani wuri da ake kira Central Square yayin da suke tsaye a hanyar da aka kebe domin tafiyar kafa.

Nan take tirjiya da kai komo ta barke, inda ‘yan sandan suka harbe mutumin, wanda suka bayyana yana dauke da wuka.

‘Yan sandan dai izuwa yanzu ba su da hakikanin masaniyar dalilin da ya sa mutumin ya yi wannan aika aika, amma sun ce b asa zargin wannan aika-aika na da alaka da ayyukan ta’addanci.

Da alamun mutumin ya yi wannan aika-aika ne shi kadai, ‘yan sandan sun ki tabbatar da rahotan kafar yada labarai da ya bayyana mutumin na da tabin hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG