Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Najeriya Sun Cafke Masu Aikata Miyagun Laifuka


Yansandan Najeriya Ta Yi Nasarar Cafke Wasu Masu Aikata Miyagun Laifuka

Shelkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar cafke gungun masu aikata miyagun laifuka a sassa daban daban na kasar.

Da yake gabatar da rukuni na farko na masu sacewa ko kwace motoci daga Najeriya su kai kasar Nijar su sayar, Kakakin yansandan Najeriya Frank Mba yace wannan gungun masu aikata laifi suna amfani da na'urar hana gane inda suke.

Mba yace wannan shine karo na biyu a tarihin satar motoci a Najeriya da ake samun barayin motoci na amfani da fasahar zanani wajen hana gano inda suke.

"Ya zuwa yanzu kuma sun saci motoci Talatin, ko da yake rundunar 'yan sanda ta musamman karkashin jagorancin DCP Abba kyari sun gono wasu daga cikin motocin."

Mba yace wannan shine karo na biyu a tarihin satar motoci a Najeriya da ake samun barayin motoci na amfani da fasahar zanani wajen hana gano inda suke.

Sai gungu na biyu kuma da aka kama wani limamin coci mai suna Pastor Adetokunbo Adetoku shi da wasu mukarrabansa biyu da laifin yin garkuwa da wani ma'aikacin kamfanin aikewa da sakonni.

Mutumin ya kawo wani sako ne na wani kaya da limamin majami'ar ya saya ta internet daga nan kuma sai suka yi garkuwa da shi bayan sun yi masa allurar barci, sai suka ajiye shi a wani ginin karkashin kasa dake cikin cocin.

Sannnan sai gungu na uku na wani kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi da ya dawo daga kasar Afirka ta kudu, ya zo ya kafa wata kungiyar yin garkuwa da mutane.

"Odeferi Chikeze ya yi ta tafka ta'asa har ta kai 'yan sanda na nemansa ruwa a jallo, inda a bara ya gudu zuwa kasar Togo. Bayan ya dawo ne a wannan shekara 'yan sanda suka kame shi."

Ya shaidawa manema labarai cewa yana karban kudin fansa daga Naira milyan uku, milyan biyu zuwa Naira milyan daya. Ya ce kudin fansa da ya karba ya karasa gina gidansa da ya fara ne lokacin yana Afirka ta kudu sannan ya sayi dalleliyar motar alfarma Lexus Jeep.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG