Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sandan Najeriya Sun Cafke Wani Gungun 'Yan bindiga


An cafke Wasu Gungun Yan Dindiga Dadi 30.

Hedkwatar Rundunar Yan sandan Najeriya ta ce zaratan dakarunta sun cafke wasu gungun yan bindiga dadi kimanin su talatin da takwas.

Da yake nunawa yan jaridu gungun yan bindigar a Abuja, kakakin Rundunar Yan sandan kasar DCP Frank Mba, ya ce an kame yan bindigar ne a sassan arewa maso yamma, arewa maso gabas da arewa ta tsakiya.

An dai kwato manyan bindigogi kirar AK47 guda ashirin da hudu, harsasai Dubu shida da kuma wasu Karin bindigogi kirar gida guda goma sha biyar. Kana da wasu kananan bindigogi kirar Pistols na kwarai. Guda ashirin.

Wannan nasara dai da Yan sandan suka cimma yazo daidai lokacin da yankin arewacin Najeriyar ke ci gaba da fuskantar matsalar tabarbarewar tsaro

Masanin tsaro wing commander musa isa salman Wanda yace wannan nasara na Yansanda na karfafa gwiwa ya nemi da suke kuma bada karfi wajen tattaro bayanan sirri don Kara cimma nasara.

Domin Karin Bayani Saurari Rahoton Hassan Maina Kaina

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG