Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Najeriya Sun Kashe Mutum 24 A Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Ta Watan Agusta - Amnesty


Zanga-zangar tsadar rayuwa a babban birnin Abuja.
Zanga-zangar tsadar rayuwa a babban birnin Abuja.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce binciken da ta yi kan yadda hukumomin Najeriya, suka murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Agusta, ya nuna cewa jami’an kasar sun kashe akalla masu zanga-zangar 24 tare da tsare wasu fiye da 1,200.

Rahoton mai shafuka 34 da Amnesty International ta fitar a ranar Alhamis, ya samo asali ne daga shaidun gani da ido da hirarraki da ma’aikatan lafiya da iyalai da abokan wadanda abin ya shafa.

Amnesty ta ce 'yan sandan Najeriya sun yi amfani da karfin tuwo kan masu zanga-zangar da suka taru domin nuna adawa da tsadar rayuwa.

Ta ce 'yan sanda sun kashe akalla mutane 24, ciki har da yara biyu. An samu asarar rayuka a fadin jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da kuma Neja.

A cewar rahoton, ‘yan sanda sun yi ta harbe-harbe kai tsaye a kusa da kan wadanda lamarin ya rutsa da su, yayin da wasu da abin ya shafa suka shaki hayaki mai sa hawaye.

Isa Sanusi, darektan kungiyar Amnesty a Najeriya, ya yi imanin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sosai.

“Ko a yau da muke kaddamar da wannan rahoto a Kano, iyalai da dama sun fito suna shaida mana cewa ‘ya’yansu sun bace, wasu da dama kuma ana kyautata zaton an kashe su ko kuma ana tsare da su a asirce, don haka batun gaba daya ya fi yadda ake tsare da su. Wannan kawai ya nuna cewa hukumomin Najeriya ba su shirya amincewa da cewa jama’a na da ‘yancin yin zanga-zangar lumana ba.”

Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, wadda masu shirya ta suka kira "Ranaku Goma na Fushi", ta kasance mayar da martani ne ga tsadar rayuwa da mutane da dama suka yi imani da cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi ne ya haifar da su, ciki har da cire tallafin man fetur.

Hukumomin ‘yan sandan Najeriya ba su mayar da martani kan zargin Amnesty ba, amma a baya sun musanta yin amfani da harsashi mai rai wajen dakile zanga-zangar.

Kakakin ‘yan sandan kasar bai amsa kiran da Muryar Amurka ta yi masa ba.

A cikin watan Oktobar 2020, zaluncin 'yan sanda ya haifar da zanga-zangar adawa da Rundunar ‘yan sandan SARS.

Zanga-zangar dai ta kawo karshe ne sakamakon harbi da bindiga da aka yi a kofar karbar harajin Lekki da ke Legas.

Najeriya dai ta dade tana fama da ta’asar ‘yan sanda, duk kuwa da alkawuran da aka sha yi mata na cewa za ta kara kaimi.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG