Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sandan Pakistan Sun Kama Wasu da Suka Yiwa Wata Yarinya Tsiraici


'Yan sandan Pakistan

Wasu mutane sun shiga hannun 'yan sandan kasar Pakistan bayan da suka tube wata 'yar shekara 16 da haihuwa tsirara kana suka zagaya kauyensu da ita a matsayin ramuwar gayya

Jami’an ‘yan sandan Pakistan sun kama wasu maza takwas bisa tsamani ko kuma zargin sun da yiwa wata yarinya ‘yar shekaru 16 da haihuwa tsirara, suka kuma zagaya kauyensu da ita, a zaman ramuwar gayya, bayan da suka zargi dan uwanta da laifin zubar da mutunci gidansu domin ya yi huldar da bai kamata ba da ‘yar uwarsu.

An ragewa shugaban ‘yan sandan yankinmukaminsa bayan da binciken, ya nuna cewa, shi ya fadawa yarinyar abin da zata fada, ya kuma canza mata maganarta ta farko.

Shafin yanar gizo na gidan talabijin din GEO ya rawaito yarinyar na cewa “ta fuskanci barazana daga ‘yan sanda, wanda hakan yasa ta kasa fadin gaskiyar abin da ya faru da ita. Tace an tilasta mata fadin abubuwan da bata so fadi ba,”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG