Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Sake Kamo 'Yan Bindigan Da Ke Zargin Alaka Da Sanata Melaye


Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Najeriya
Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Najeriya

Mutane shidan da aka ce sun tsere daga ofishin 'yan sandan Lokoja da ake zarginsu da aikata manyan laifuka cikinsu harde mutane biyu da aka ce Sanata Melaye ne ya basu makamai.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta samu nasarar sake cafko mutanen nan guda shida da suka arce daga ofishin 'yan sandan dake Lokoja a daidai lokacin da ake shirin kaisu gaban kotu.

Cikin wadanda aka sake kamowa har da mutanen nan biyu da suka ce Sanata Dino Melaye ne ya basu bindigogin da ake zarginsu da mallaka ba bisa ka'ida ba.

Tun a makon jiya ne aka bada rahoton mutanen sun tsere daga ofishin na 'yan sandan jihar Kogin a birnin Lokoja. Wannan alamarin ya sa babban sifeton 'yan sanda na kasa ya kori kwamishanan 'yan sandan jihar Kogi.

Kakakin 'yan sandan na jihar Kogi ASP Williams Aya, ya tabbatar wa Muryar Amurka da sake kama mutanen, a lokacinda aka tuntube ta wayar tarho inda ya ce tuni suka mika mutanen zuwa Abuja inda zasu fuskanci shari'a. Yace a cikin jihar Kogi din aka kama mutanen.

Amma masu sharhi akan alamura a jihar ta Kogi sun nuna shakku akan tserewar mutanen tunda farko. Malam Muhammad Bashir mazaunin Lokoja yana cikin masu shakka. Ya ce duk rufa rufa ne domin a nemi hanyar da za'a musgunawa Sanata Melaye. A cewarsa bayanan 'yan sandan suna cin karo da juna. Ya ce dama sun san za'a sake kamasu din ne. Tun farko ma ba tserewa suka yi ba, an dai kaisu wani wuri an ajiyesu kana yanzu an ce an sake cafkosu.

Malam Bashir Muhammad ya ce nan gaba mutanen zasu fada a kotu cewa Sanata Melaye ne ya sa suka tsere daga inda ake tsare dasu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG