Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Senegal Sun Yi Zanga-zanga Saboda Karancin Wutar Lantarki


Masu zanga-zanga a birnin Dakar

An barke da zanga-zanga a fadin Dakar, babban birnin kasar Senegal da yammacin jiya Litini saboda karancin wutar lantarki.

An barke da zanga-zanga a fadin Dakar, babban birnin kasar Senegal da yammacin jiya Litini saboda karancin wutar lantarki. ‘Yan sanda sun ce masu zanga-zangar sun kona tayu suka kuma wargaza komai a ofisoshin gwamnati da kuma ofishin hukumar wutar lantarkin kasar, mai suna Senelec.

Yan sanda da shaidun gani da ido sun bayar da rahoton kone-kone a sassan birnin Dakar. A wasu lokutan har said a ‘yan sanda su ka yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zangar.

Wannan zanga-zangar, ta zo ne bayan wata da aka yi a makon jiya saboda yinkurin Shugaba Abdoulaye Wade na yin kwaskwarima wa kudin tsarin mulkin kasar. ‘Yan adawa da dama na fargabar cewa kwaskwarimar za ta say a iya sake cin zabe cikin sauki, sannan ya kuma ya dora dansa a kan layin zama shugaban kasa. Mr. Wade dai ya janye shawarar canza kundin tsarin mulkin tun ma kafin Majalisar kasar ta kada ku’i'a a kai.

Wutar lantarki ta yi ta dada tabarbarewa a Senegal kuma hakan kan faru na tsawon kwanaki ma a wasu sassa, wanda hakan ke gurgunta tattalin arzikin kasar.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG