Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Somaliya tayi bukin cika shekaru 51 da samun 'yancin kai


Firai Ministan kasar Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed

Gwamnatin kasar Somaliya tace bukin samun yancin kai na bana, lokaci ne da kasar da yaki ya daidaita zata shata wani sabon babi na zaman lafiya.

Gwamnatin kasar Somaliya tace bukin samun yancin kai na bana, lokaci ne da kasar da yaki ya daidaita zata shata wani sabon babi na zaman lafiya. Manyan jami’an gwamnatin ne suka shiga bukin daga tutocin a fadar shugaban kasar dake Mogadishu yau da safe, na cika shekaru 51 da samun ‘yancin kai a Somaliya. Kakakin sabon PM Abdiweli Mohamed Ali ya bayyana cewa, bukin na bana ya nuna cewa an sami raguwar tashin hankali a kasar. Abdirahaman Yarisow yace sakin jiki da mutane suke yi suna tafiya kan tituna da sanyin safiya alama ce cewa, murkushe mayakan al-Shabab da gwamnati ke yi yana tasiri. Sai dai ‘yan kasar Somaliya dake kasashen ketare sun musanta haka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG