Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Shi'a Na Kiran Gwamnatin Da Ta Sako Malamin Su


Sheik Ibrahim El-Zakzaky

Magoya bayan jagoran kungiyar mabiya mas-habar Shi'a Shekh Ibrahim El-Zakzaky, dake birnin Legas sun kara jaddada kiran su ga gwamnatin Najeriya data hanzarta sako jagoran nasu domin neman magani, la’akari da raunin da ya samu a hannun jami’an tsaro a lokacin da aka kama shi.

A wani taron manema labarai da 'yan kungiyar daga yankin kudu maso
yanmacin Najeriya suka gudanar a legas, sun ce abin takaici shi ne duk
da cewar kotuna da alkalai daban daban, sun umarci jami’an tsaro su sako
malamin nasu da iyalan sa, da kuma biyan shi diyya, har yanzu gwamnatin
Najeriya da jami’an tsaron sunyi watsi da wannan umar ni.

Malam Abdullahi Mohammed Musa, na daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi wajen wannan taro na manema labarai.

Kungiyar Shi'a dai, kungiya ce da sauran al’ummar musulmai ke musu kallon
wadanda suka kauce daga tafarkin sunnah, da kuma neman tada zaune tsaye, sai dai a cewar mabiyan, wannan rashin fahimta ce.

Malam Mohammed Sani ya ce, tun a shekara ta 2016 ne dai wani alkalin kotun tarayya a Abuja, ya bada umarnin jami’an tsaro su saki Malam Ibrahim El-Zakzaky, da uwargidan sa. Ya kuma bayyana cewa cigaba da tsare shin da hukumomi keyi haramun ne.

Sai dai hukumomi sun ce suna tsare dashi ne domin kare lafiyar sa da kuma tabbatar da tsaro.

Ga rahoton wakilin muryar Amurka Salihu Jibril.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG