Accessibility links

'Yan Siyasa Zasu fara kamfen zaben shugaban kasa a Venezuela

  • Grace Alheri Abdu

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Venezuela suna layi suga gawarsa
‘Yan siyasar kasar Venezuela suna shirin kamfe gadan-gadan domin zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar goma sha hudu ga watan Aprilu na maye gurbin Hugo Chavez, shugaban dan gurguzu wanda ya rasu makon jiya bayan ya yi fama da cutar sankara na lokaci mai tsawo.

Hukumar zaben kasar Venezuela ce ta sanar da ranar zaben jiya asabar, kwana daya da zaben mataimakin Mr. Chavez, Nicolas Muduro a matsayin magajinsa aka kuma rantsar da shi shugaba mai rikon gado.

Yana yiwuwa gwamnan jihar Miranda Henrique Capriles ya tsaya takara da Mr. Maduro. Mr. Chavez ya kada shi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktoba bara.

Mr. Capriles yace rantsar da Mr. Muduro da aka yi ranar jumma’a a ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Shugabanin kasashen latin America 18 da kuma sauran shugabannin kasasshen ketare suka halarci jana’izar Mr. Chavez ranar jumma’a. Amurka ta tura wata tawagar jami’an diplomasiya.
XS
SM
MD
LG