Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Ba Zasu Tsorata Mu Ba-Boubacar Keita


Ibrahim Boubacar Keita

Shugaban Kasar Mali Boubacar Keita yace 'yan ta'adda ba zasu tsorata al'mmar kasar ba, duka da hare haren da ake fuskanta a kasar

Shugaban kasar Mali Boubacar Keita ya fada jiya asabar cewa, harin rashin imani ba zai firgita mutanensa ba, bayanda wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe akalla mutane goma sha hudu a harin da aka kai wani sansanin soji.

An kaiwa sansanin sojin da yake garin Soumpi, wanda ke tsakiya kasa kusa da kan iyaka da yankin Timbuktu na kasar Mali hari da asuba. Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin harin.

Mayakan tsaurin ra'ayin addinin Islama sun kwace ikon yankunan hamada dake in arewacin kasar a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu kafin bayan shekara daya, aka kakakbe su daga wurin karkashin jagorancin Faransa.

Sai dai duk da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka girke, da kuma dakarun dake aiki karkashin wani shirin kakkabe mayaka na Faransa, ana ci gaba da samun karuwa tashin hankali da hare hare a kudancin kasar kusa da Bamako babban birnin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG