Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takara 28 Zasu Fafata A zaben Shugaban Kasa A Kamaru


Shugaban Kamaru - Paul Biya

'Yan adawar kasar Kamaru sun gaza gabatar da dan takara daya tilo da zai iya fafatawa da shugaban kasar Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 36 yana mulkin kasar. Yan takara 28 zasu fafata a zaben shugaban kasa na ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ake sa ran Biya zai lashe.

Mai karancin shekaru a cikin yan takarar zaben ranar 7 ga Oktoba, dan jarida ne mai suna Cabral Libi. Kafin ya gabatar da sunasa a matsayin dan takara, dan shekaru 38 yace yana tababa ko zai iya yin takarar, saboda ba zai iya samar da kudin da hukumar zabe ta bukaci ga kowane dan takara, wanda ya kai dalar Amurka dubu 60. Yace sai da ya nemi magoya bayansa su taikama masa.

Yace ya tabbatar da shi ne dan takara daya tilo da yake da karfin fafatawa da shugaban kasa mai ci Paul Biya saboda ya yi kokari ya samu wannan kudi dala dubu 60 a hannun magoya bayansa tsakanin kwanaki uku, ya biya hukumar zabe kamar yanda dokokin kasar suka bukaci ga kowane dan takara.

Kasar Kamaru ta dade tana fama da hare haren mayakan Boko Haram da kungiyoyin awaren kasar na yankuna Ingilishi guda biyu da kuma rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake shigo mata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG