Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Amurka Sun Koma Fafutikar Neman Zabe


Clinton ta jam'iyyar Democrat da Trump na jam'iyyar Republican

Yan’ takarar shugaban kasa Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat da Donald Trump na jam’iyyar Republican, sun koma fagen yakin neman zabe bayan yan kwanaki masu cike da fadi tashin siyasa, ciki har da zazzafar muhawara da suka yi ranar Lahadi, da kuma kalaman batsa game da mata da Trump yayi, da gagarumin rabuwar kawuna da aka samu tsakanin ‘yan jam’iyyar ta Republican, da kuma bullar batun wasikun email na Mrs Clinton wanda ya nuna tana bakin ganga.

Duka ‘yan takarar biyu suna kokarin shawo kan rashin yarda da masu kada kuri’a suke nunawa ana kasa da wata guda a gudanar zaben shugaban kasar Amurka.

Kakakin majalissar wakilai Paul Ryan, ya fadawa wakilai ‘yan jam’iyyar Republican a wani taro da aka yi jiya Litinin cewa, ba zai kara yi wa Trump kemfe ba, ko ya kare irin magangunansa marasa dadi da yake yi wadda ke batawa masu kada kuri’a rai.

Ryan ya ce maimakon haka, zai maida hankali akan ganin an zabi ‘yan jam’iyyar Republican a majalissar wakilai domin jam'iyyar ta ci gaba da xama mai rinjaye amajalisun dokokinn Amurka. A yanzu haka dai ‘yan jam’iyyar ta Republican ne ke rike da majalissar wakilai da ta datijjai

Mutum daya daga taron na jiya ya fadi cewa Ryan bai janye goyon bayansa ga Trump ba, amma dai ba zai yi masa yakin neman zabe ba, Ryan kuma ya fadawa sauran ‘yan Republican dake majalissar cewa “ ku yi abinda kuka ga zai kaiku ga samun nasara.”.

XS
SM
MD
LG