Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka Sun YI Muhawara Ta Biyu


Shugaban Amurka Barack Obama (D) yana amsa tambaya daga wani daga cikin jama'a a gaban dan takarar jam'iyar Republican Mitt Romney (H)
Shugaban Amurka Barack Obama da abokin hamayyarsa na jam’iyar Republican Mitt Romney fafata kan tattalin arziki da makamashi da tsare-tsaren kasashen kasashen ketare a muhawara ta biyu a kamfen neman zabe, inda suka amsa tambayoyin Amurkawan da basu tsaida shawara kan wadanda zasu zaba ba a wani salon zabe na tattaunawa kai tsaye da masu kada kuri’a da aka gudanar a jami’ar Hofstra dake birnin New York.
Romney ya kushewa shugaba Obama kan aikin da ya gudanar cikin shekaru hudu da suka gabata da cewa, ya ruba gibin kasafin kudin kasar kuma bai gudanar da aikin da yace zai yi ba. Yace "kawo yanzu matsayin rashin aikin yi zai ragu zuwa kashi biyar da digo hudu bisa dari. Banbancin halin da ake ciki da kashi 5.4% shine Amurkawa miliyan tara basu da ayyukan yi. Ba nine nace kashi 5.4% ba. Wannan ne tsarin shugaba Obama amma bai kai wurin ba. Yace kawo yanzu zai gabatar da tsarin kula da lafiyar tsofaffi da tsarin fansho domin ya bayyana cewa, suna dab da durkushewa. Har yanzu bai gabatar da wani shirin a kan ko da daya daga ciki ba."

Shugaba Obama ya maida martani da cewa, ya cika galibin alkawuran da ya yi, yace wadanda bai cika ba, ba wai domin bai dauki wani mataki a kai bane. Yace "Shekaru hudu da suka shige na shaidawa Amurka cewa zai ragewa masu matsakancin karfin albashi haraji, na kuma yi. Na ce zan ragewa kananan harkokin kasuwanci haraji, Na yi haka. Nace zan kawo karshen yakin Iraq. Nayi. Nace zan maida hankali kan wadanda suka kai harin ta’addanci sha daya ga watan tara, mun kuma yi farautar shugaban al-Qaida fiye da yadda aka taba yi kuma Osama bin Laden ya mutu."

‘Yan takarar biyu sun kuma fafata kan shirin fitar da Amurka daga koma bayan tattalin arziki cikin shekaru hudu masu zuwa. Yayinda suka kuma yi bayanai kan batun shige da fice da harin da aka kai ofishin jakadancin Libya da kuma tsarin makamashin kasar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG