Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka Sun YI Muhawara Ta Karshe


Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Republican Mitt Romney yana bayani yayinda shugaba Barack Obama ke sauraro
Shugaban Amurka Barack Obama da abokin hamayyarsa na jam’iyar Republican Mitt Romney sun bayyana raunin juna yayin muhawararsu ta uku kuma ta karshe, inda shugaba Obama yace Mr. Romney ya yi kuskure a dukan ra’ayoyinsa kan tsare tsaren harkokin kasashen ketare.

Tsohon gwamnan jihar Massachussets ya maida martani a muhawarar da aka yi a Florida da cewa, kushe masa ba shine matakin shawo kan tashin hankalin da ake yi a gabas ta tsakiya ba.

Mr. Romney ya kushewa tsare tsaren kasashen ketare na Mr. Obama a yankin da cewa, ya ga “akasin irin makomar da muke begen gani a yankin”

Na jinjina masa da kashe Osama bin Laden da kuma farautar shugabannin kungiyar al-Qaida, amma ba zamu warware wannan matsalar ta wajen daukar matakin soja ba. Tilas ne mu samar da kyakkyawaan tsari da zai taimaki kasashen Musulmi da sauran kasashen duniya, domin ganin sun nisancin irin wannan tsaurin ra’ayin wanda babu shakka baya tafiya ko ina. Ba a boye yake ba.

Mr. Obama ya bayyana cewa, Amurka tana hada kai matuka da abokan kawancenta wajen wanzar da zaman lafiya da kafa damokaradiya a yankin, ya kuma yi misali da Libya.

Ba tare da girke dakaru a kasar ba, kuma a cikin kasa da kudin da aka kashe cikin mako biyu a Iraq, muka ‘yantar da kasar da ta shafe shekaru 40 karkashin mulkin kama karya, muka hambare mutumin da ya kashe Amurkawa, kuma duk da wannan bala’in da ya auku, kaji dubban Libiyawa sun fita bayan abinda ya faru a Bengazi suna cewa, “Amurka abokiyar kawancenmu ce. Muna tare da ita.”

A kan Iran kuma, Mr. Obama yace gwamnatinsa ta nuna karfinta ta wajen kakabawa Iran takunkumi mafiya tsauri da aka taba kakabawa jamhuriyar Islaman a tarihinta.
Mr. Romney a nasa bangaren yace, ya rage “shekaru hudu” duniya ta kai lokacin da Iran zata mallaki nukiliya” ya kara da cewa, shugabannin kasar Iran suna ganin gazawa a inda suke kyautata zaton ya kamata Amurka ta nuna karfinta.

Da aka tambaye shi ko menene yake gani yafi barazana ga Amurka, sai yace ayyukan nukiliyan kasar Iran.

Yayinda Mr. Obama yace kungiyoyin ta’addanci sune har yanzu babbar barazana ya kara da cewa, tilas ne mu ci gaba da zama da tsaro.
XS
SM
MD
LG