Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Takarar Shugabancin Amurka Sun Mayar Da Hankalinsu Kan Wasu Jihohi


Hillary Clinton da Donald Trump

Baki daya ‘yan takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat da Donald Trump na jam’iyyar Republican sun mayar da hankalinsu akan wasu jihohi da suke bukatar ganin sun sami nasara a kansu.

A gobe Talata ne ake sa ran gudanar da babban zaben Amurka mai cike da dinbin tarihi. Muryar Amurka ta tuntubi tsohon ma’aikacinta kuma mazaunin Amurka, Shehu Yusif Kura, don jin inda aka kwana a shirye shiryen zaben dake tafe.

Shehu Yusif Kura, yace jam’iyyar Democrat ta mayar da hankali wajen ganin ta samu nasara a jihar Pennsylvania, domin yanzu haka ‘yar takarar Hillary Clinton da mijinta Bill Clinton da kuma ‘yarsu Chelsea Clinton da shugaban kasar Amurka Barack Obama da uwargidansa zasuyi wani gagarumin taro a jihar, wanda hakan ke nuna muhimmancin wannan jiha ga jam’iyyar Democrat.

Haka kuma Hillary zata je jihohin da suka hada da Michigan da North Carolina da kuma New Hampshire, shi kuma shugaba Obama zai ziyarci wasu jihohi biyu da suka da New Hampshire da kuma Michigan domin yakin neman zabe.

A daya bangaren kuma, Shehu Kura, cewa yayi dan takara Donald Trump ya fara kame kame domin ya zuwa yanzu ya hakura da zuwa jihar Pennsylvania, domin yana ganin cewa jihar tayi masa nisa, inda ya canza zuwa ‘daya daga cikin jihohin Minnisota da Michigan da kuma North Carolina.

Saurari cikakkiyar hira da Shehu Yusuf Kura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG