Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Taliban Sun Kai Hari Kan Ofishin Jakadancin Amurka da NATO


Wasu 'yan jarida a tsaye kusa da wata motar da aka yiwa kaca-kaca da harsashai a lokacin da ake kan kai harin birnin Kabul a ranar Talata13 ga watan Satumba

'Yan tawayen Taliban sun afkawa NATO da ofishin jakadancin Amurka da kuma hukumar leken asirin Afghanistan a birnin Kabul

Mayakan Taliban sanye da rigunan tayar da bama-baman kunar bakin wake, kuma dauke da gurnetocin da ake harbawa da rokoki, sun kai hari a tsakiyar birnin Kabul, ciki har da hedikwatar NATO, da Ofishin Jakadancin Amurka da kuma hukumar leken asirin Afghanistan.

An yi ta jin amon wuta da karar bama-bamai a babban birnin Afghanistan har zuwa yau Talata, a yayin da jami’an tsaro ke kokari fatattakar maharan su yi nisa da shiyyar gine-ginen diflomasiyyar birnin. Hukumomi sun ce wani dan sanda da wasu mayakan sa kai biyu sun hallaka.

‘Yan sandan Afghanistan sun ce mahara wajen biyar ne su ka kwace wani babban benen da ake kan ginawa a dandalin Abdul Haq da ke Kabul, sannan su ka shiga bude wuta kan muhimman wurare.

'yan sandan kasar Afghanistan
'yan sandan kasar Afghanistan

NATO ta ce wani karamin gungun mayakan sa kai sun kai hari kan harabar Ofishin Jakadancin Amurka da kuma hedikwatar dakarun gamayya, sannan su ka yi ta bude wuta daga waje. Dakarun Afghanistan da na NATO sun mayar da martani, ta yadda dakarun gamayyar su ka hada da jiragen yaki.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Kabul ya tabbatar da faruwar harin na yau Talata daura da harabarsa mai samin tsauraran matakan tsaro, to amma ofishin ya ce babu wani ma’aikacinsa da ya sami rauni. Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka Kerri Hannan, ta ce an umurci ma’aikata da su nemi mafaka.

Wani mai magana da yawun Taliban ya gaya wa kafafen yada labarai cewa manyan wuraren da 'yan tawayen su ka tassama su ne hukumar leken asirin Afghanistan da wata ma’aikata, da ofishin jakadancin Amurka da kuma NATO.

Babban magatakardan kungiyar kawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen ya gayawa manema labarai a birnin Brussels cewa ba ya shakka sojojin kasar Afghanistan na iya magance al'amarin da ya faru a birnin Kabul. Haka kuma ya ce irin wadannan hare-hare ba za su hana NATO ta mikawa sojojin Afghanistan ragamar tafiyar da ayyukan tsaron kasar ba. Shugaban kungiyar ta Nato ya ce an kama turbar yin hakan kuma ba fashi.

XS
SM
MD
LG