Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tura Jakadunta Gabas Ta Tsakiya Kan Batun Kafa Kasar Falasdinu


Wani mai zanga zaga yake nuna dantsen hanu da aka yi wa fenti da alamun tutar Falasdinu.

Gwamnatin shugaban Amurka Barack Obama ta tura manyan jakadunta biyu zuwa Gabas ta tsakiya a kokarin da take yi na kaucewa fito na fito kan bukatar yankin falasdinu na amince da kafa kasar.

Gwamnatin shugaban Amurka Barack Obama ta tura manyan jakadunta biyu zuwa Gabas ta tsakiya a kokarin da take yi na kaucewa fito na fito kan bukatar yankin falasdinu na amince da kafa kasar.

Bisa dukkan alamu tattakin da jakada David Hale, da wani babban jami’in fadar White House Dennis Ross zasu yi, ana ganin wan nan shine matakin karshe na kokarin shawo kan falasdinu kada ta gabatar da bukatar kafa kasa ga Majalisar Dinkin Duniya, a lokacin taronta na shekara shekara makon gobe birni New York, matakin da Isra’ila take matukar adawa dashi.

Wani babban jami’in yankin Falasdinu Moahmmed Shtayyeh, ya fada jiya talata cewa kasarsa zata nemi cikakkiyar amincewar majalisar na kafa kasa.

Amma sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta sake gargadin cewa tattauna kai tsaye tsakanin Isra’ila da Falasdinu ce kadai hanyar da zata kai ga samun zaman lafiya mai dorewa a yankin. Clinton tace jakadu Hale da Ross, zasu gana da PM Isra’ila Benjamin Netanyahu, da shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas.

Ahalin yanzu kuma PM Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya gayawa ministocin kasashen larabawa da suke taro a Alkahira cewa Ankara zata goyi bayan yunkurin yankin Falasdinu na neman kafa kasar mai ‘yancin gashin kai. Ya kira matakin da cewa abu ne “wajibi ” ba wai ana da zabi akan haka ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG