Accessibility links

'Yan tawayen Abzinawa Sun Gana Da Mai Shiga Tsakani Na ECOWAS


Mayakan kungiyar 'yan tawayen neman 'yancin Azawad ta 'yan kabilar Abzinawa a kasar Mali, zaune cikin motarsu a wata kasuwa dake Timbuktu a kasar Mali, a watan Afrilun 2012.

Shugabannin Abzinawan sun ce ba wai 'yancin kai na nufin ballewa daga kasar Mali baki daya ba ne, kuma ba su yarda da 'yan kishin addini ba

Wata kungiyar ‘yan tawaye mai neman kafa ‘yantacciyar kasa mai akidar da ba ta addini ba a arewacin Mali, ta gana a karon farko da jami’in shiga na kungiyar ECOWAS a rikicin kasar Mali.

Shugabanni uku na kungiyar kwatar ‘yancin Azawad, MNLA ta ‘yan kabilar Abzinawa, sun tattauna jiya asabar da shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso, mai shiga tsakani a rikicin.

Shi ma ministan harkokin wajen Burkina, Djibril Bassole, ya shiga cikin wannan tattaunawa da aka yi a Ougadougou babban birnin kasar Burkina Faso.

Daya daga cikin shugabannin Abzinawan, Ibrahim Ag Mohammed Assaleh, yace kungiyarsu ta yi na’am da shiga tsakani na kungiyar ECOWAS. Haka kuma yace ‘yanci ba wai yana nufin a balle yankin daga sauran kasar Mali ba ne, ana iya ba yankinsu ‘yancin tattalin arziki da na al’ada, kuma ta ci gaba da kasancewa cikin kasar Mali.

Yace ‘yan tawayen ba su yarda da duk wata kungiyar ta’addanci ko ta masu kokarin shimfida Islama a arewacin Mali ba.

A watan da ya shige ‘yan tawayen Abzinawa suka yi kokarin kulla yarjejeniya da kungiyar Ansar Dine mai alaka da al-Qa’ida domin hada karfi waje guda da nufin kafa kasar Azawad ‘yantacciya. Amma tattaunawar ta su ta wargaje a bayan da ‘yan tawayen Abzinawan suka ki yarda cewar za a yi aiki da dokokin shari’ar Musulunci ne kawai a kasar.

Gwamnatin rikon kwarya ta Mali ta ki yarda da ayyana ‘yancin da ‘yan tawaye suka yi a arewacin kasar.

XS
SM
MD
LG