Accessibility links

'Yan Tawayen Abzinawa Sun Kashe Dan Zanga Zanga A Gao.

  • Aliyu Imam

Wakilan kungiyar Ansar Dine a Ougada a wata ganawa da mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS, kuma shugaban Burkina Faso, Blaise Compaore.

Daga arewacin Mali shaidun gani da ido sun bada labarin anyi arangama tsakanin masu zanga zanga da kuma daya daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye dake iko da yankin.

Daga arewacin Mali shaidun gani da ido sun bada labarin anyi arangama tsakanin masu zanga zanga da kuma daya daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye dake iko da yankin.

Wani shugaban matasa a birnin Gao ya gayawa Muriyar Amurka cewa, kungiyar ‘yan awaren abzinawa da ake kira MNLA ta bude wuta kan kimanin mutane 200 wadan da suka yi maci zuwa helkwatar kungiyar a talatan nan.

Shugaban matasan yace an kashe akalla mutum daya, wasu 12 kuma suka jikkata, biyu daga cikinsu raunukansu suna da tsanani.

Abin da ya janyo zanga zangar itace zargin cewa kungiyar ‘yan awaren MNLA, ta kashe wani wakilli Idrissa Oumaru ranar litinin, bayan da yaki yarda a masa fashin Babur dinsa. Masu zanga zanga sunyi macin ne bayan anyi jana’izar wakili Omaru.

A cikin wata sanarwa data bayar gwamnatin wucin gadi a Mali tace kisan wakilin ya sami wuri ne domin rashin tsaro a yankunan da ‘yan tawaye suke da iko, daga nan ta sha alwashin cewa sai an hukunta wadan da suke da alhakin kashe shi.

Wakilin Muriyar Amurka da ya ziyarci yankin makon jiya, yace akwai zaman dar dar tsakanin mazauna yankin, da kuma ‘yan awaren abzinawa da ‘yan kungiyar nan mai da’awar Islama da ake kira Ansar Dine.

XS
SM
MD
LG