Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan tawayen Chadi Na Zargin Nijar Da Nuna Bangaranci A Aikinta Na Shiga Tsakani


Dakarun kasar Chadi.

Al’umomin kasar Chadi sun fara nuna damuwa a game da yadda hukumomin suka kasa bayyana matsayinsu game da bukatar mika ‘yan tawayen kungiyar Fact ga gwamnatin rikon kwarya, wadda ta fara zargin jamhuriyar Nijar da nuna bangaranci a rikicin da ake yi.

Jamhuriyar Nijar dake makwabtaka da kasar Chadi ta kasance wacce kasashen G5 Sahel suka daurawa nauyin samar da masalaha a tsakanin gwamnatin rikon kwarya ta CMT da kungiyar ‘yan tawayen FACT a washegarin rasuwar shugaba Idriss Deby.

Sa’o’i kadan bayan haka, gwamnatin rikon kwaryar Chadin ta bukaci hukumomin Nijar su tusa keyar wasu shugabanin ‘yan tawaye da take zaton sun buya a jihar Diffa, bukatar da dan kungiyar ROTAB Mahamadou Tchiroma Aissami, ke cewa alama ce dake nunin sabuwar gwamnatin ta Chadi ba ta lakanci makamar mulki ba.

Karin bayani akan: Idriss Deby, G5 Sahel, FACT, CMT, Jamhuriyar Nijar, kasar ta Chadi, da Chad.

Ya zuwa yanzu hukumomin Nijar, ba su bayyana matsayinsu ba a game da bukatar cafke ‘yan tawayen na Chadi ba, haka kuma kakakin gwamnati Minista Tidajin Abdoukadri ya ce ba za su yi furuci akai ba.

Hakan na faruwa ne duk kuwa da cewa a wata sanarwa da ta fitar a baya bayan nan, kungiyar ta FACT ta zargi Nijar da nuna bangaranci a takaddamar dake tsakaninsu da gwamnatin CMT.

Farfesa Issouhou Yahaya malamin kimiyar siyasa da tarihi ne a jami’ar Abdoul Moumouni ta Yamai, ya kuma gargadi mahukuntan Nijar su ci gaba da tsayawa a matsayinsu na masu shiga tsakani don kaucewa abin da masu iya magana ke cewa, ‘ba ka ci kasuwa ba, rumfa ta fada maka’.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG