Accessibility links

'Yan Tawayen Mali Sun Hadu, Sun Ce Zasu kafa Kasar Islama


Wani hoton da kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta kasar Mali, MNLA, ta bayar tana mai cewa mayakanta ne a wani wurin da ba ta bayyana ba a kasar.

'Yan tawayen Abzinawa da wata kungiyar Islama sun ce sun hade domin kafa kasa 'yantacciya mai bin tafarkin Islama a arewacin Mali

'Yan tawayen Abzinawa da wata kungiyar Islama mai zazzafan ra'ayi a kasar Mali sun ce sun hade domin kafa 'yantacciyar kasa mai bin tafarkin Islama a arewa.

Wannan sabuwar gamayyar ta kunshi Abzinawa na kungiyar Kwaton 'Yancin Azawad (MNLA), da 'ya'yan wata kungiya mai alaka da al-Qa'ida da ake kira Ansar Dine.

Kungiyoyin biyu sun ce sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar hadewar ranar asabar da maraice a garin Gao na arewacin Mali.

Yarjejeniyar ta bukaci kungiyoyin biyu da su hada karfi wuri guda domin kirkiro sabuwar 'yantacciyar kasa ta Azawad, wadda zata rika amfani da dokokin shari'ar Islama.

Gwamnatin rikon-kwarya ta Mali ta yi watsi da ikirarin 'yan tawayen cewa zasu mayarda yankin arewacin Mali ya zamo 'yantacciyar kasa.

XS
SM
MD
LG