Accessibility links

Mayakan sakai A Mali Sun Kama Wani Sabon Gari: Diabaly.

  • Aliyu Imam

Sojojin Mali suke binciken wata motar Fasinja a shigar Markala.
Ministan tsaron Faransa, jean-Yves Le Drian ya gayawa wata tashar talabijin ta Faransa cewa ‘yan tawayen sun kama Diabaly ne bayan da suka gwabza wani kazamin fada da da dakarun Mali.

Wakiliyar Muriyar Amurka Anne Look, wacce take Bamako, ta aiko mana da rahoton cewa rundunar sojojin Mali tana tura karin sojoji da nufin tusa keyar mayakan sakan, wadanda aka bada labarin suna dauke makamai sosai.

Garin Diabaly, yana daga arewaci da kuma tsakiyar kasar inda jiragen yakin Faransa suka kai harin bama-bamai kan sansanin horaswa na ‘yan tawayen, da kuma rumbunan adana makamai.

An bada rahotannin cewa litinin ma jiragen yakin Faransa sun kai karin farmaki a tsakiyar kasar.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana wani zama na musamman a ranar litinin din nan, bisa bukatar da Faransa ta gabatar ganin yadda lamarin yake kara tsanani.
XS
SM
MD
LG