Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Tijjaniyya Sun Bukaci ‘Yan Izala Su Bar ‘Ya’yansu Su Rika Yin Wazifa A Jami’o’i 


Taron Shekara Na Kungiyar ‘Yan Tijjaniyya A Najeriya
Taron Shekara Na Kungiyar ‘Yan Tijjaniyya A Najeriya

Kungiyar 'yan boko ta Tijanniyya wato "International Tijjaniyya Burotherhood" ta bukaci 'yan Izala su bar 'ya'yan kungiyar su sakata su wala wajen yin wazifa a masallatan jami'o'i.

ABUJA, NIGERIA - Kungiyar dai da ke da malamai da dalibai 'yan Tijjaniyya a jami'o'in Najeriya, ta bayyana korafin ne a taron ta na shekara- shekara a Abuja.

Taron Kungiyar ‘Yan Tijjaniyya Na Shekara A Najeriya
Taron Kungiyar ‘Yan Tijjaniyya Na Shekara A Najeriya

Taron wanda ya samu halartar kungiyar dalibai ta 'yan Tijjaniyya a jami'o;i wato TIMSAN ya nuna Tijjanawan ba su samu karfin da su ke bukata a kungiyar dalibai Musulmi na makarantun Najeriya ba da hakan ya sa a ke daukar wasu ayyukan ibada na 'yan Tijjaniya sun wuce gona da iri.

A bayaninsa, Farfesa Muhmmad Mustapha Gwadabe na jami'ar Ahmadu Bello ya ce kalubalen ya shafi dalibai ne amma ba hukumomin jami'a ba.

Farfesa Muhammad Mustapha Gwadabe na ABU Zaria lokacin da ya halarci taron ‘yan kungiyar Tijjaniyya na shekara
Farfesa Muhammad Mustapha Gwadabe na ABU Zaria lokacin da ya halarci taron ‘yan kungiyar Tijjaniyya na shekara

Shi ma shugaban kungiyar dalibai na TIMSAN Muhmmad Auwal daga jami'ar Ilorin ya nuna su akidar Sufanci su ke kai da Shehu Ibrahim Niasse ya jaddada.

Taron wanda ya gudana a masallacin kasa na Abuja ya samu halartar Tijjanawa maza da mata daga sassan Najeriya.

Wasu Da SUka Halarci Taron Kungiyar ‘Yan Tijjaniyya Na Shekara A Najeriya
Wasu Da SUka Halarci Taron Kungiyar ‘Yan Tijjaniyya Na Shekara A Najeriya

Yayin da Salafawa ko 'yan Izala a Najeriya ke sukar Sufawa da aikata bidi'a, Sufawa na cewa a'a a bar mu su akidar su don ba kowace bidi'a ce bata ba.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

‘Yan Tijjaniyya Sun Bukaci ‘Yan Iza Da Su Bar ‘Ya’yan Su Yin Wazifa A Jami’o’i .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG