Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Uwan Fasinjojin da Aka Sace Sun Tabbatar Da Sahihancin Bidiyon Da Ke Yawo Yanar Gizo


Jirgin Kasa
Jirgin Kasa

Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald da ya shiga tsakanin 'yan-bindiga da iyalan mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna, Malam Tukur Mamu da kuma 'yan-uwan wadanda aka sacen sun tabbatar da sahihancin faifan bidiyon da ke yawo a yanar gizo inda 'yan-bindiga ke dukan mutanen.

Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu ya ce faifan bidiyon da gaske ne sai dai duk da haka ya ce ba zai kara tsoma baki akan maganar sakin mutanen ba sai idan gwamnati ta sauya salo.

Malam Mamu ya ce cigaba da shiga tsakanin 'yan-bindigan da kuma 'yan-uwan wadanda aka sacen na da matukar hadari saboda haka ba zai sake tsoma baki ba sai idan gwamnati ta nuna da gaske ta ke yi kuma ta shiga maganar tukuna.

A hirar shi da Muryar Amurka, Malam Sani Lawal daya daga cikin 'yan'uwan wadanda ke hannun 'yan-bindigan har yanzu ya bayyana cewa ya ga 'yan-uwan shi a cikin wannan faifai.

Ya ce “ba mu taba shiga halin kunci da damuwa irin na ganin wannan faifan bidiyon ba saboda haka mu na cikin damuwa matuka da irin halin da 'yan-uwan mu ke ciki a daji”.

Kimanin watanni hudu kenan dai da sace wadannan mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna kuma har yanzu saura kusan mutane 43 cikin sama da sittin da aka sace da farko.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

XS
SM
MD
LG