Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Falasdinawa Sun Kashe Mutane Hudu A Israila


 Avigdor Lieberman, sabon ministan tsaron Israila
Avigdor Lieberman, sabon ministan tsaron Israila

'Yanbindiga Falesdinawa guda biyu sun bude wuta kan wasu mutane wadanda suke sayayya da wadanda suke cin abinci kusa da ma'aikatar tsaron Israila a birnin Tel Aviv jiya Laraba suka kashe mutane hudu tare da raunata wasu biyar.

'Yansandan Israila sun bayyana harin a zaman harin ta'adanci kuma sun ce 'yanbindigan sun yi anfani da bindigogi ko kuma makamai masu sarrafa kansu da kansu.

Haka kuma 'yansandan Israila sun cafke maharan. Daya daga cikin 'yanbindigan yana kwance a asibiti sanadiyar harbeshin da aka yi. 'Yansanda sun kara da cewa maharan 'yanuwan juna ne da suka fito daka garin Hebron na gabar yammacin kogin Jordan.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka da kakkausan lafazitayi Allah wadai da harin wanda ta bayyana a zaman aikin matsorata akan farar hula da basu san hawa ba , basu san sauka ba

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG