Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yancin Addini, Muhimmin ‘Yanci


White House
White House

'Yancin addini, kamar kowane' yancin ɗan adam, abu daya ne a duniya kamar yadda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana yayin fitowar Rahoton Sashen 'Yancin Addini Na Kasa da Kasa na shekara-shekara.

“Dukan mutane, a ko’ina, suna da ‘yanci ko a ina suke zaune, abin da suka yi imani da shi, ko abin da ba su yarda da shi ba. . . . Ba za a iya samun cikakken 'yanci na addini ba sai dai idan an mutunta wasu' yancin ɗan adam, kuma idan gwamnatoci suka take hakkin al’ummarsu na yin ibada, hakan na jefa sauran cikin haɗari. "

Ga mutane da yawa a duniya, har yanzu basu da 'yancin addini. A zahiri, a cewar Cibiyar Bincike ta Pew, ƙasashe 56 suna takurawa mai tsanani kan 'yancin addini.

Gwamnatin Iran na ci gaba da tsoratarwa, musgunawa, da kame mambobin kungiyoyin addinai marasa rinjaye, wadanda suka hada da mabiyan Baha’is, Kiristoci, Yahudawa, da kuma mabiya addinin gardajiya Zorotawa, da Musulman Sunni da Sufi.

A Burma, shugabannin juyin mulkin soja suna daga cikin wadanda ke da alhakin kisan kare dage da sauran munanan dabi'u kan Musulmin Rohingya.

A Rasha, hukumomi na ci gaba da musganawa, tsarewa, da kwace dukiyoyin mabiyan Jehovah’s witness da membobin kungiyoyin Musulmi marasa rinjaye bisa zargin tsattsauran ra'ayi.

Saudi Arabiya ta kasance kasadaya tilo a duniya da ba ta da dakunan ibadarkirista, duk da cewa akwai kiristoci sama da miliyan da ke zaune a Saudiyya. Kuma Jamhuriyar Jama'ar China a fili take saka hukuncin laifi ga duk mabiya addini kuma tana ci gaba da aikata laifukan cin zarafin bil'adama da kisan kare dangi kan Musulman Uighurs da mambobin sauran kungiyoyin addini da kabilu marasa rinjaye a China.

Wasu kasashen na daukar matakai don kara girmama 'yancin gudanar da addini, in ji Sakatare Blinken: “Shekarar da ta gabata, gwamnatin rikon kwarya da farar hula ta jagoranta a Sudan ta soke dokokin ridda da dokar kasa da aka yi amfani da ita wajen musgunawa mambobin kungiyoyin addini marasa rinjaye.

Gwamnatin Uzbekistan ta saki daruruwan mutane da aka daure saboda imaninsu. . . .Turkmenistan ta saki mabiyan Jehovah’s witness 16 da suka ki shiga soja saboda imaninsu. ”

Za mu kula da dadaddenjagorancin Amurka kan 'yancin addini, in ji Sakatare Blinken, kuma za mu ci gaba da aiki tare da masu rajin kare hakkin dan adam da kuma kungiyoyin addinai don yakar dukkan nau'ikan.

XS
SM
MD
LG