Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yankin Catalonia Ya Bukaci Kasar Spain Ta Tattauna Da Shi.


SPAIN - Demonstrators hold Spanish and Catalonian flags as they take part in a rally to mark Spain's National Day in Barcelona, northeastern Spain, 12 October 2017

Shugaban yankin Catalonia Charles Puidgemont yace majilsar zata ayyana yancin wannan yanki muddin gwamnatin kasar Spaniya taki ta tattauna da ita.

Shugaban yankin Catalonia, Carles Puidgemont, ya fada yau cewa, majalisar yankin zata kada kuri’ar ayyana 'yancin wannan yanki idan gwamnatin Spaniya taki tattaunawa a maimakon haka ta aiwatar da barazanarta ta kwace ‘yancin cin gashin kan da yankin ke da shi.

PM Mariano Rajoy yaba Pudgemont wa’adin zuwa safiyar yau alhamis ya bayyana ko ya riga ya ayyana ‘yanci a yankin bayan kuri’ar raba gardamar da aka kada farkon watan nan.

Puidgemont ya ayyana ‘yancin yankin a kaikaice a jawabin da ya gabatar makon da ya gabata, sai dai yace ya dakatar da daukar mataki a hukumance domin bada damar tattaunawa da gwamnati a birnin Madrid. Ya bayyana matsayinsa a wata wasika da ya rubuta yau alhamis ana dab da cikar wa’adin da aka dibar masa.

Nan da nan ofishin Rajoy ya maida martani da cewa, yana shirin wani taron majalisar zartarwa na musamman ranar asabar da nufin aiwatar da sashe na dari da hamsin da biyar na kundin tsarin mulkin kasar Spain da yaba gwamnati janye ikon cin gashin kan yankin.

Masu kada kuri’a a Cataloniya sun zabi ‘yantar da yankin a zaben raba gardamar da aka gudanar ranar daya ga watan Oktoba, sai dai kasa da rabin wadanda suka cancanci kada kuri’a suka gudanar da zabe, yayinda masu adawa suka kauracewa zaben. Gwamnatin Rajo tayi watsi da kuri’ar raba gardamar da tace ta sabawa doka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG