Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa,'Yansandan kasar Sun Kama Wani Matuki Da Yake Shirin Afkawa Mutane.


 'Yansanda suke aiki a wani lamari na daban.
'Yansanda suke aiki a wani lamari na daban.

Matukin bai sami damar tsallake shingayen da aka gindaya a kofar masallacin ba.

‘Yan sandan kasar Faransa sunce an kama wani mutum da yake kokarin afkawawa gungun mutane da mota a kofar wani masallaci dake garin Cretiel. Babu wanda yaji rauni a lamarin jiya alhamis.

Direban da ba a bayyana ba, bai iya wuce shingayen da aka kafa kewayen masallacin ba, bisa ga cewar ‘yan sanda.

Jaridar Le Parisien ta buga rahoto cewa, yana neman ramuwar gayya ne kan harin da kungiyar IS ta kai, da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Paris kwanan nan.

Makon da ya gabata, aka kashe wani mutum da dama kuma suka jikkata, lokacin da wata babbar mota ta kutsa kan wadansu da suka je aikin ibada, daidai sun tashi daga wani masallaci a birnin London.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG