Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

''Yansanda Tara Masu Fashi da Makami da Sace Mutane Sun Shiga Hannu


IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Kakakin rundunar 'yansandan Najeriya dake Abuja yace sun cafke wasu 'yansanda tara da ake zargi da hannu a fashi da makami tare da sace mutane suna garkuwa dasu domin samun kudin fansa.

Rundunar ta gano bindigogi kirar AK47 guda goma sha hudu da harsashai 363 tare da karin wasu miyagun makamai a hannun 'yansandan dake hada baki da bata gari.

Kazalika rundunar ta kara cafke wasu daban masu sace mutane domin neman kudin fansa. Su ma din an samu makamai guda goma tare da su. 'Yansandan sun fada da bakinsu cewar su ne suke samar ma bata garin abubuwan fashewa kamar su bam a jihohin Legas da Ogun.

A shiyar arewa maso gabas rundunar 'yansandan tace ta kara cafke wasu tsoffin 'yansanda da suke taka rawa wurin tada hankali a yankin. Yanzu dai an gane cewa yawan fashi da makami da sace mutane dake aukuwa akwai hannun 'yansanda ciki.

AIG Ibrahim Baba Ahmed tsohon mataimakin babban sifeton 'yansanda ya bada dalilin da ya sa ake samun wasu 'yansanda suna hada baki da bata gari. Yace dansandan Najeriya na cikin mawuyacin hali. Na daya ba'a biyansa albashin kirki. Nera dubu ishirin da bakwai babu abun da zata yiwa mutum. Haka kuma ana turasu aiki amma basu da kayan aiki. Ko a ofishin 'yansandan babu motocin aiki haka kuma bindigoginsu na ya ku bayin Allah ne.

Baba Ahmed yace idan ana son kasa ta gyaru to wajibi ne a kula da dansanda.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG