Speto Janar na ‘Yan sandan Nigeria Ibrahim Idris, ya tura tawagar jami’an ‘Yan sandan kwantar da tarzoma su dari biyar akan hanya tsakanin Abuja da Kaduna domin magance matsalar sata da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Rundunar wacce take karkashin jagorancin mukaddashin speto janar na ‘Yan sanda DIG Joshak Habila, zata kunshi harda ‘Yan sandan ciki.
Matsalar garkuwa da mutane tayi tsanani a baya baya nan kan hanyar Abuja zuwa kaduna, inda ko makon jiya sai da aka yi zargin barayi sun yi awon gaba da mutane 20, wadanda uku daga cikinsu aka sako su bayan da aka biya kudin fansa.
Da yake Karin bayani kan aikinsu, mukaddashin speto janar Habila yace, aikinsu shine kawo karshen wannan fitina.
Da yake amsa tambayar abunda yasa aka sami koma bayan tsaro kan hanyar tunda aka daina amfani da tashar jirgin sama dake kaduna, DIG Habila yace, waccar runduna aikinta daban, duk da haka yana bada tabbaci ba zasu yi kasa a guiwa ba.
DIG Habila ya yarda cewa rashin biyan jami’an ‘Yan sanda wasu hakkokinsu yana daga cikin wasu dalilai da suke kawo koma baya a aikinsu.
Ya bada tabbacin cewa helkwatar ‘Yan sanda tana kokarin ganin an biya jami’an tsaro hakkokinsu.
Facebook Forum