Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Ingila Sun Tsare Wasu Matasa Bisa Zargin Shirin Ta'addanci

PM Britaniya David cameron a ciki wani shirin BBC.

‘Yansandan ingila sunce sun tsaida wasu mutane biyar da suka tuko motarsu, suka tasarwa wata ma’aikatar sarrafa makaman nukiliya dake arewa-maso-yammacin Ingilar.

‘Yansandan ingila sunce sun tsaida wasu mutane biyar da suka tuko motarsu, suka tasarwa wata ma’aikatar sarrafa makaman nukiliya dake arewa-maso-yammacin Ingilar.

Daman PM Ingila din, David Cameron ya riga ya gargadi mutanen Biritaniya da su zauna cikin halin shiri saboda sa-ran hare-haren maida martani kan kashe madugun al-Qaida Osama Bin Laden da aka yi.

Rundunar ‘yansanda ta Cumbria tace tana tsare da wadanan mutanen biyar wadanda dukkansu matasa ne ‘yan shekaru ashirin-ashirin, kuma tuni ma aka kwashe su zuwa Manchester inda ‘yansandan yaki da ta’addanci ke ci gaba da yi musu tambayoyi.

XS
SM
MD
LG