Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar White House tace Bin Laden baya dauke da makamai lokacin da aka kashe hi


Kakakin fadar White House James Carney yana gabatar da John Brennan, mashawarcin Shugaba Barack Obama kan yaji da ta'addanci a wani taron manema labarai

Fadar White House ta ce shugaban al-Ka’ida Usama bin Laden, bai dauke da makami a lokacin da dakarun Amurka na musamman su ka kashe shi a Pakistan ran Litini.

Fadar White House ta ce shugaban al-Ka’ida Usama bin Laden, ba ya dauke da makami lokacin da dakarun Amurka na musamman suka kashe shi a Pakistan ranar Litini. Sai dai kakakin Fadar White House Jay Carney ya gayawa manema labarai jiya Talata cewa bin Laden ya nuna turjiya ga dakarun ruwa na SEAL da suka kai hari a gidan da ya ke boye. Carney ya ce ai ita turjiya ba sai da makami ake yinta ba, amma bai bada karin bayani ba. An dai gano mutumin da aka fi nema a duniya din ne, a wani gida na kimanin dala miliyan guda a arewa da Islamabad, babban birnin Pakistan. Carney yace an harbi bin Laden ne a ka da kuma kirji. Yace an harbi daya daga cikin matan bin Laden a kafa, amma ba a kashe ta ba, a yayin da ta abkawa dakarun na Amurka. Kakakin na Fadar White House ya ce za a yanke shawara kan ko ya dace, ko kuma za a iya, bayyana hotunan yadda aka kai harin. A halin da ake ciki kuma, Carney ya ce hukumomi na fatan bayanan sirrin da aka tattara a gidan za su bayyana duk wani shirin kai hari, da kuma bayanai game da wasu muhimman batutuwa, da kuma wadanda su ka dauki nauyin bin Laden a Pakistan. Daraktan Hukumar Leken Asirin Amurka (CIA) Leon Panetta, ya yi bayani ga ‘yan Majalisar Wakilai da na Dattawan Amurka a kebe jiya Talata. A wata hirar da ya yi da mujallar Times, Shugaban na CIA yace Amurka ta yanke shawarar yin gaban kanta sabili da gudun kada hukumomin Pakistan su ankarar da Osama Ba a sanar da gwamnatin Pakistan ba game da kai harin, har sai lokacin da jirage masu saukar ungulun suka bar sararin samaniyarta.

XS
SM
MD
LG