Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan majalisar dokokin Amurka sun harbi wani mutum jiya Linin


Ginin majalisun dokokin Amurka da ake kira Capitol
Ginin majalisun dokokin Amurka da ake kira Capitol

Wani mutum da ya shiga harabar majalisar dokokin Amurka cikin masu yawon bude ido ya samu mugun rauni yayinda 'yansandan dake binciken masu shiga ginin suka bude masa wuta saboda ya fitar da bindiga zai harbesu

Mutumin mai suna Larry Dawson dan shekaru 66 da haihuwa ya fito daga jihar Tennessee ne.

Yanzu dai yana asibiti inda yake samun jinya saboda mugun raunin da ya samu yayinda ake cigaba da bincike.

Shugaban 'yansandan majalisar Chief Matthew Verderosa yace wata mace dake tsaye kusa da mutumin ta samu rauni wanda bashi da muni. Babu kuma wani jam'in 'yansandan da ya ji rauni.

Shugaban 'yansandan yace wani babban laifi ne mutumin da ya saba ziyarar majalisar ya yi ba shirin ta'adanci ba ne.

Ko watan Oktoban bara an caji Dawson da laifin tada hankalin jama'a a harabar ginin majalisar lokacin da ya kaima wani dansanda bugu a zauren majalisar wakilai yana daga murya tare da karanta wasu ayoyi daga littafin Bible da ikirarin cewa shi waliyi ne.

Da aka gurfanar dashi gaban kotu ana gargadeshi kada ya kara zuwa harabar majalisar. An cigaba da shari'ar amma bai bayyana a kotu ba a watan Nuwamba.

Jiya Litinin duk majalisun biyu na hutun Easter. Basu yi zama ba. Amma akwai dubban masu yawon bude ido a harabar majalisun

XS
SM
MD
LG