Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu a Amurka Za a Rika Tsare Mata Bakin Haure Masu Ciki


 Shugaba Trump
Shugaba Trump

A cigaba da sauye-sauye da Shugaban Amurka Donald Trump ke yi a bangaren shigi-da-fici, yanzu za a rika tsare mata bakin haure masu ciki.

Shugaban Amurka Donald Trump ya soke wani tsari na tsohuwar gwamnatin-Obama, wanda ya hana jami’an shigi-fici tsare mata masu ciki da ake shirin kora daga kasar.

Daga yanzu, za a saki mace mai ciki ne kawai, idan jami’an Kwastam da na Shigi-da Fici su ka ga hakan ya dace saboda irin yanayinta.

A tsarin baya, bakin haure mata masu ciki, wadanda ke fuskantar kamu, akan yadda a sake su bisa sharadin beli ko kuma saka ido. To amma Shugaba Donald Trump ya bayar da umurnin a cigaba da tsare karin bakin haure mata masu ciki, ya ce hujjarsa kuwa ita ce ana sakinsu da yawa, kuma sam basu gurfana wajen sauraron shari’ar tasa keyarsu.

Wannan canjin tsarin, jami’an shigi da fici ne su ka aika shi ga Majalisar Dokokin kasar da safiyar jiya Alhamis, sannan daga baya kuma aka bayar da sanarwar hakan a wata hira ta waya da manema labarai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG