Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom A Mota Ya Tashi Potiskum


A yanzu yanzun nan muka sami labarin fashewar wani bom a harabar ofishin ‘yan sanda dake Potiskum, wanda yayi sanadiyar mutuwar ‘yan sanda biyu da raunata a kalla mutane biyar.

Na zanta da Mallam Zakari Adamu shugaban rundunar adalci na jihar Yobe, inda ya shaidamin cewar wani mutum ne aka ganshi a mota kusa da kasuwar mtn, wanda gurine da mutane ke harkar kasuwanci dakuma tashar motoci a gurin, da mutane suka ganshi yana zirga-zirga sai basu yarda da shi ba, har suka kira masa ‘yan sanda, wanda aka kamashi zuwa ofishin ‘yan sanda domin bincikar sa an kuma ajiye shi a bayan kanta, aka kuma dauko motarsa zuwa ofishin domin bincike.

Alokacin da ake bincikar motar ne missalin karfe hudu saura bom ya fashe a motar wanda yayi sanadiyar mutuwar ‘yan sanda biyu a nan take da raunata mutanen dake kusa da gurin. Kuma an nemeshi an rasa bayan fashewar bom din.

XS
SM
MD
LG