Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Kunar Bakin Wake Ta Tsallake Rijiya da Baya


Yarinya Zahra Mai Bom

Wata yarinya da aka tura ta aiwatar da kunar bakin wake a kasuwar Kwari dake Kano ta fada hannun mahukunta.

Yayin da ake yi mata tambaya ta ambaci sunanta a matsayin Zahra kuma tace ta fito ne daga jeji wanda bata san inda yake ba.

Tace wasu mutane ne da ba iyayenta ba suka turata yin aikin. Da suka isa Kano wai sai aka tsayar da babur irn mai kafafu uku sai suka shiga suka je kasuwa. Su uku ne mata. An gaya masu idan sun shiga kasuwar rarrabuwa zasu yi. Idan ta farko ta tayar da bam Zahra da wata kuma sai su tayar da nasu.

Da suka shiga kasuwar sai dayar tace su tayar sai ita Zahra ta ki. Amma waccan ta tayar da nata wanda ya jima Zahra ciwo. Da ta tashi sai ta samu wani babur tace ya kaita Dawanau domin ita da iyayenta sun taba zama wurin. Asalinta Damaturu jihar Yobe.

Daga Dawanau aka samu wani dattijo ya kaita asibiti da nashi babur din na shiga. Har an fara yi mata aiki sai dattijon ya dawo yace ya gano wata jaka cikin babur din wadda ta yarinyar ce. Tace bam ne ke cikin jakar kuma nata ne.

ASP Magaji Musa Majiya kakakin 'yan sandan Kano yayi karin bayani. Yace Zahra Babangida daga jihar Bauchi aka kawota Kano tare da wasu zuwa kantin Kwari. Bam ya tashi da sauran matan biyu amma Allah ya hana nata tashi.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG