Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Nelson Mandela Ta Mutu


Zindzi Mandela

Zindzi Mandela, ‘yar shahararren masu fafutukar yaki da launin fata a Afirka ta Kudu Nelson da Winnie Mandela ta mutu a Johannesburg tana da shekaru 59 a duniya. 

Kafar yada labaran kasar ta SABC ta sanar cewa Mandela ta mutu a wani asibiti da ke babban birnin Afirka ta Kudu amma basu bayyana sanadin mutuwarta ba.

Jam’iyyar African National Congress mai Mulki wanda mahaifinta ya jagoranta a gwagwarmayar kawar da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudun ce ta tabbatar da mutuwarta.

Nelson Mandela da matarsa Winnie
Nelson Mandela da matarsa Winnie

A shekara ta 1985 Zindzi ta yi fice, lokacin da ta karanto wasikar da mahaifinta ya rubuta ta kin amincewa da sharadin samun ‘yancin kai da shugaba P.W. Botha ya bayar na ANC ta watsi da dabarunta masu tsauri akan nuna addawa ga wariyar launin fata.

Mandela na aiki a matsayin jakadiyar Afirka ta kudu a kasar Denmark a lokacin da ta mutu.

Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandor, ta yabawa Zindzi Mandela tana mai cewa ”a matsayinta na diyar gwarzon gwagwarymaya Tata Nelson da Mama Winnie, ita kanta jaruma ce a fagen gwagwarmaya. Ta yi wa Afirka ta Kudu aiki sosai."

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG