Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Na Taimakawa A Yaduwar COVID-19 - WHO, UNICEF


WHO - World Health Organization
WHO - World Health Organization

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kuma hukumar UNICEF, sun yi gargadin yara ‘yan shekara 12 abin da yayi sama su rika sanya abin rufe baki da hanci kamar yadda manya suke yi, yayin da ‘yan shekara 11 zuwa kasa kuma su rika sanyawa a wuraren da ke da hatsari, domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Yara da suka girma sun fi saurin yiwuwar yada cutar fiye da kanana a cewar hukumomin biyu, inda suka kara da cewa akwai bukatar kara fadakar da jama’a akan yadda yara kanana suke iya taimakawa wajen yaduwar kwayar cutar mai haifar da COVID-19.

WHO da UNICEF suka ce yanayin da ya kamata yara manya su saka takunkumin shi ne inda ba’a iya tabbatar da samun tazarar mita daya ko kafa uku tsakaninsu da wasu, da kuma yanayin yawaitar kamuwa da cutar acikin al’umma.

Hukumomin sun yi kira ga iyaye da su tabbatar da yaransu sun sami takunkumin na rufe baki da hanci, da kuma yin amfani da shi, kana kuma su lura da matakin kamuwa da cutar a yankunansu, manya su kuma rika lura da sanya ido sosai akan kanana.

To sai dai hukumomin na WHO da UNICEF sun ce yara ‘yan kasa da shekaru 5 ba su bukatar saka takunkumin.

Yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ta coronavirus ya kai 800,000 ya zuwa ranar Assabar, a cewar jami’ar Johns Hopkins, wadda kuma ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya ya haura miliyan 23.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG