Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yar'adua Shugaba Ne Na Hakika - Jonathan


Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da matarsa

Shekaru shida ke nan da Allah ya yiwa tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa Yar'adua rasuwa, rasuwar da ta kaiga mataimakinsa Goodluck Jonathan daga yankin Niger Delta ya dare kan mulki

A wata budaddiyar wasika da ya rubuta a shafinsa na Facebook tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan wanda ya gaji Yar'adua ya yi masa fatar aljanna fiddaushi.

Goodluck Jonathan ya bayyana Umaru Musa Yar'adu a matsayin jan gwarzo wanda ya shugabanci Najeriya bilhaki da gaskiya. Ya jinjina masa a shekarun da ya kwashe yana mulkin Najeriya.

Alhaji Garba Wazirin Yaba wani dan asalin jihar Katsina ya yiwa Muryar Amurka karin haske game da marigayi Umaru Musa Yar'adua. Yace su ba zasu manta da abun da ya yi masu ba a jihar Katsina da ma Najeriya baki daya. Saidai dan Najeriya mantuwa gareshi. Duk dan Najeriya ya san shugaba Yar'adua ya dauko hanyar gyara kasar. Misali ya gyarawa yansanda da sojoji albashinsu yadda za'a rabasu da cin hanci da rashawa.

Matsa ma sun tuna da tsohon shugaban. Wani matashi yace Yar'adu ya yi ayyuka da dama musamman lokacin da yake gwamna har ma ya gina jami'a. Ya bunkasa harkokin ilimi tare da ba kowane yaro ilimi kyauta da kayan karatu kyauta. Ya gina hanyoyi da dama.

A zamanisa ne aka kirkiro da ma'aikatar kula da cigaban yankin Niger Delta. Shi ne kuma ya fito da shirin yiwa tsagerun Niger Delta din ahuwa tare da biyansu albashi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG