Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Yemen


Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Saudiya Adel al-Jubeir
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Saudiya Adel al-Jubeir

Amurka ta shirya yarjejeniyar tsagaita wuta na kwana biyar da Saudiya a farmakin da take kaiwa Yemen sabili da aikin jinkai.

Mayakan Houthi a Yemen sun bayyana yin na’am da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana biyar bisa dalilan jinkai,bisa shawarar kasar Saudi Arabiya da za a fara gobe Talata.

Sanarwar ta jiya Lahadi ta zo ne ‘yan sa’oi bayanda jiragen yakin dakarun hadin guiwa da Saudi Arabiya ke jagoranta suka kai hari kan gidan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh a Sana’a babban birnin kasar. Ana kyautata zaton tsohon shugaban kasar baya gida a lokacin da aka kai harin, daga baya kuma aka nuna shi a talabijin yana tsaye gaban baraguzan gidan.

Makon jiya, Amurka da Saudi Arabiya suka sanar da shirin tsagaita wuta a Yemen, inda dakarun hadin guiwa karkashin jagorancin Saudiya suke kai farmaki ta sama kan mayakan Houthi dake arewacin kasar da suka mamaye wadansu sassan kasar cikin ‘yan watannin nan.

Jiya Lahadi Sarkin Saudi Arabiya Salman, ya kare matakin sojin da kasar ta dauka da yace shugabannin kasar Yemen suka bukaci ayi, da nufin ceto kasar Yeman din da al’ummarta daga abinda ya kira ‘kungiyar kasashen ketare” dake barazana ga dorewar yankin.

XS
SM
MD
LG